Saudiya

An soke dokar da ta hana bude shaguna a lokutan Sallolin jam'i a Saudiya

Yerima mai jiran gado na Saudiya, Mohammed Ben Salman.
Yerima mai jiran gado na Saudiya, Mohammed Ben Salman. AP - Bandar Aljaloud

Saudiyya ta amince a hukumance  shaguna su ci gaba da kasancewa a bude a lokutan salloli 5 na Musulmai, a wani sauyi mai sarkakiya da kasar ke yi don tsamo kanta daga matsalar tattalin arziki.

Talla

Tun da ya zama Yarima mai jiran gado na kasar a shekarar 2017, Mohammed bin Salman ya gabatar da sauye sauye na tattalin arziki da zamantakewa da ya tsara da zummar rage yawan dogaro da danyen mai da kasar ke yi.

A wata sanarwa, hukumar cinikayya ta  Saudiyya ta ce  z a ci gaba da harkokin tattalin arziki a gaba daya ranakun aiki, musamman a lokutan salloli na kowace rana.

Wannan sabuwar dokar ta cire da duk wani shamaki a game da kasuwanci da cinikayya , wanda hkumomin kasar suka ce yana janyo wa tatalin arziki asarar biliyoyin Riyals.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.