Isra'ila-Fasaha

An bankado manhajar da ke tatsar bayan masu wayar salula

Kafafen jaridu sun bankado yadda ake makala manhajar Pegasus a cikin wayar fiattun mutane domin sace bayanansu na sirri.
Kafafen jaridu sun bankado yadda ake makala manhajar Pegasus a cikin wayar fiattun mutane domin sace bayanansu na sirri. Chris DELMAS AFP/File

Ana zargin wani kamfanin Isra’ila da yi wa dubban mutane leken asiri ta hanyar makala wata boyayyiyar manhaja a cikin wayoyinsu na salula, yayin da bayanai ke cewa, fitattun ‘yan jarida da masu gwagwarmaya da attajirai da ‘yan siyasa na cikin wadanda aka yi musu leken asirin.

Talla

Da ma dai, an jima ana zargin kamfanin na NSO da sayar wa da gwamnatocin kasashen duniya manhajar leken asiri ta Pegasus, wadda ake amfani da ita wajen bibiyar halin da mutun ke ciki na sirri.

Manhajar na iya kunna kyamarar wayar salular mutun ko kuma makirhonta tare da tattaro bayanan da ke kunshi a cikin wayar ba tare da saninsa ba.

Wasu kafafen jaridu da suka hada da The Washington Post da The Guardian da Le Monde da sauransu, su ne suka bankado irin leken asirin da wannan kamfani ke yi wa jama’a a madadin wasu gwamnatocin kasashe, abin da ya haifar da fargaba game da ‘yancin mutun na killace sirrinsa.

Jaridun sun bankado cewa, sama da wayoyin zamani dubu 50 ne a sassan duniya, aka makala musu wannan manhajar tun daga shekarar 2016.

Kodayake kamfanin na NSO ya musanta wannan zargi, yana mai bayyana shi a matsayin tsagwarar karya.

Kazalika gwamnatocin kasashen duniya sun fara fitowa daya bayan daya suna musanta zargin da ake yi musu na amfani da manhajar wajen kwashe bayanan masu yi musu adawa a gida da waje.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.