Saman Jannati

Burin attajirin duniya Bezos ya cika a yau

Jeffe Bezos a kusa da kumbon Blue Origin da kamfaninsa ya kera
Jeffe Bezos a kusa da kumbon Blue Origin da kamfaninsa ya kera - BLUE ORIGIN/AFP/Archivos

Shugaban kamfanin Amazon, Jeff Bezos tare da abokan aikinsa guda uku sun samu nasarar sauka a duniyar wata bayan tsawon shekaru 20 da aka dauka ana fafutukar ganin wannan rana.

Talla

A yau Talata, Bezos, da dan uwansa, Mark Bezos, da wata matukiyar jirgin sama Wally Funk tare da wani dalibin kasar Holland Oliver Daemen, kumbonsu ya samu damar sauka a inda suka nufa.

Kamar dai yadda bayanai ke cewa jirgin ko kuma kumbon da ya lula da su na da girma sosai, wanda kamfanin Bezos ya kera, karon farko da ya yi jigila zuwa sama jannati.

Jirgin wanda ya tashi daga Arewacin Texas da ke Amurka, ya yi tafiyar tsawan kilomita 100 kwatankwacin Mil 62, kafin ya tsallaka wata duniyar.

Kumbon dai na dauke da wata mata mai suna Funk 'yar shekaru 82 mafi tsufa da ta taba zuwa duniyar wata a tarihi, sai Daemen mai shekaru 18 wanda ya kasance mafi karancin shekaru da ya taba tsallake wannan duniyar.

Bezos ya dade da bayyana sha'awar zuwa wannan wuri, yana mai cewa labarin zuwa duniyar wata ya sauya rayuwarsa kuma ya bashi kwarin gwiwar neman zuwa wannan duniyar da ba tamu ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.