fARANSA - KUTSE

Pegasus: Macron na daga cikin wadanda ake bibiyar wayoyinsu

Shugaban Faransa Emmanuel Macron, 20 ga watan Yuli 2020.
Shugaban Faransa Emmanuel Macron, 20 ga watan Yuli 2020. AP - John Thys

Shugaba Emmanuel Macron na daga cikin manyan jami’an gwamnatin Faransa 14 da aka yi amfani da manhajar leken asiri ta Pegasus da ake kerawa a Isra’aila don bibiyar abubuwan da ke faruwa a wayoyinsu  na sadarwa.

Talla

Jaridar Le Monde da ake bugawa a Faransa ta ce daya daga cikin lambobin wayar da shugaba Marcon ke amfani da ita, da ta tsohon firaministansa Edouard Philippe da wasu ministocinsu 14 na daga cikin wadanda ake yi wa leken asirin tsawon lokaci.

Jaridar ta ce wani kamfani mai zaman kansa da ke kasar Maroko ne ke gudanar da wannan aiki na leken asiri kan manyan jami’an gwamnati, da suka hada da ministan harkokin wajen Jean-Yves Le Drian da na kudi Bruno Le Maire, da tsohon ministan cikin gida Chritophe Castner har ma da wasu ‘yan majalisar dokoki.

Shugabannin Afirka

A nahiyar Afirka ma akwai shugabannin kasashen da lamarin ya shafa ciki har da Cyril Ramphosa da kuma Sarkin Marokoa Mohammed na 6.

Lambar wayar da ake zance, shugaba Macron ya fara amfani da ita ne tun shekara ta  2017, to sai dai bayanai sun ce hatta Sarkin Maroko Mohammed na 6 bai tsira daga masu leken asirin ba.

Forbidden Stories da kuma Amnesty International sun ce sun samu lambobin wayoyin mutane akalla dubu 50 da aka saurari wayoyinsu daga shekara ta 2016 kawo yanzu ta hanyar amfani da manhajar ta Pegasus da Isra’ila ke kerawa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.