Coronavirus

Sabon nau'in korona na Delta zai mamaye kasashen duniya - WHO

Shugaban Hukumar Lafiya ta Duniya Tedros Adhanom Ghebreyesus, watan Yuli 2021.
Shugaban Hukumar Lafiya ta Duniya Tedros Adhanom Ghebreyesus, watan Yuli 2021. © KEYSTONE/MARTIAL TREZZINI sda-ats

Hukumar Lafiya ta Duniya ta yi gargadi kan cewar sabon nau’in annobar korona na Delta na shirin mamaye kasashen duniya cikin makonni masu zuwa fiye da sauran takwarorinsa muddun aka gaza daukar matakan da suka dace.

Talla

Cikin sanarwa da Hukumar Lafiya ta Duniyar ta fitar wannan Talata, tace sabon nau’in cutar korona na Delta, wanda ya fara bulla a kasar Indiya, yanzu haka ya yadu zuwa kasashen duniya 124, kuma sama kashi uku cikin hudu na masu dauke da cutar a kasarin manyan kasashen duniya Deltan ce.

Sanarwar humuar ta Mako-mako tace, sabon nau’in Delta da ke da kaifin yaduwa fiye da kima, zaiyiwa sauran takwarorinsa zarra wajen mamaye duniya cikin watanni masu zuwa.

Sabbin nau'ukan korona

Daga cikin wasu sabin nauyin cutar da aka samu bullarsu bayaga asalin coronavirus da aka sani ta China, akwai karin wasu nau’uka da suka kara bulla, da suka hada da Alpha da aka fara ganowa a Birtaniya da yanzu ya yadu zuwa kasashe 180, da Beta da aka fara ganowa a Afirka ta Kudu, da ke cikin kasashe 130, sai kuma Gamma da ya bulla a Brazil da ke cikin kasashe 78.

WHO tace cikin makonnnin 4 na baya-bayan nan zuwa ranar 20 ga watan Yulin da muke ciki sabon nau’in Delta na kara yaduwa tamkar wutar daji, inda ya zarta kashi 75 a kasarin kasashe da ya bulla.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.