Coronavirus

Masu dauke da korona a Amurka da Caribbean sun zarta miliyan 40

Sashin gobe da nisa na asabitin Florecio Varela, ranar 13 ga watan Afrilu 2021.
Sashin gobe da nisa na asabitin Florecio Varela, ranar 13 ga watan Afrilu 2021. AFP - RONALDO SCHEMIDT

Adadin mutanen da suka harbu da annobar korona a yankin Latin Amurka da Caribbean sun zarce miliyan 40 a wannan Asabar.

Talla

Alkaluman hukumomin yankin na nuna cewa tun bayan bullar cutar a shekarar 2019 zuwa safiyar ranar Asabar, jummular masu dauke da cutar a yankin ya kai miliyan 40 da dubu 073 da 507.

Yayin da wadanda cutar ta kasashe a nahiyar ya akai kai miliyan 1 da 353 da 335.

Sakamakon yadda sabon nau’in cutar na Delta ke Yaduwa tamkar wutar daji, ya sa adadin wadanda suke dauke da cutar a duniya miliyan 192 da 942 da 266, kana miliyan 4 da 143 da 687 suka mutu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.