Isra'ila - Falasdinawa

Matashin Falasdinu da sojin Isra'ila suka harbe a Yamma da Kogin Jordan ya mutu

Falasdinawa masu zanga-zanga yayin da suke taimaka wa wani wanda aka ji wa rauni a arangama tsakaninsu da dakarun Isra'ila a kauyen Beita.
Falasdinawa masu zanga-zanga yayin da suke taimaka wa wani wanda aka ji wa rauni a arangama tsakaninsu da dakarun Isra'ila a kauyen Beita. JAAFAR ASHTIYEH AFP

Wani matashi Bafalasdine ya mutu sakamakon harbin sa da sojojin Isra’ila suka yi a yayin wata zanga- zangar adawa da matsugunan Yahudawa da ake ginawa ba bisa ka’ida  ba a yankin yamma da kogin Jordan da Isra’ila ta mamaye, kamar yadda hukumomin Falasdinawa suka sanar a jiya Asabar.

Talla

Ma’aikatar lafiya ta Falasdinu ta ce  Mohammed Munir al-Tamimi, mai shekaru 17 wanda ya yi fama da raunukan harbin bindiga ya mutu a asibiti, kwana daya bayan tarzomar da ta tashi a kauyen Beita.

Kungiyar agaji ta Red Crescent ta ce Falasdinawa 320 ne suka ji rauni a tarzomar, cikin su har da 21 da aka harba da harsashen kwarai, 68 da harsashen roba, yayin da sauran kuma hayaki mai sa hawaye ne ya yi ajalinsu.

 Hukumomin Isra’ila sun ce dakarun kasar sun mayar da martani ne ga cin zarafinsu da masu zanga- zangar suka yi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.