Sauyin yanayi

Kasashen duniya na nazari kan magance sauyin yanayi

Kasashen duniya na kokarin rage fitar da hayaki mai gurbata muhalli.
Kasashen duniya na kokarin rage fitar da hayaki mai gurbata muhalli. AP - Sam McNeil

Kimanin kasashen duniya 200 na gudanar da taro ta kafar bidiyo da zummar cimma matsaya kan wani rahoton kimiya na Majalisar Dinkin Duniya da ake kyautata zaton zai taimaka wajen magance matsalar dumamar yanayi.

Talla

Shugaban Hukumar Kula da Yanayi na Duniya, Petteri Taalas ya shaida wa mahalarta taron na wakilan gwamnatocin kasashen duniya kan dumamar yanayi wato IPCC cewa, tattaunawarsu na da muhimmanci domin kuwa, tagomashinta zai shafi wani makamancin taron sauyin yanayi da za a gudanar nan da watan Nuwamba a Glasgow.

A ‘yan makwannin  nan, an samu mummunan yanayin zafi da ambaliyar ruwa da kuma fari a nahiyoyin duniya, lamarin da ya kara zaburar da mahukunta daukar matakin magance matsalar ta dumamar yanayi.

Shugabar Kwamitin Yaki da Sauyin Yanayi na Majalisar Dinkin Duniya, Patricia Espionasa ta ce, da ma tun shekaru biyar da suka gabata, suka yi gargadi game da aukuwar wadannan bala’o’i da ake gani a yanzu.

Yanzu haka wakilan kasashen na duniya da ke halartar taron ta kafar intanet,  za su yi nazarzi mai zurfi kuma dalla-dalla kan shafuka 20-30 na rahoton kafin su mika shawarwarinsu  ga hukumomi don daukar mataki na gaba.

Taron nasu zai dauki tsawon makwanni biyu suna gudanarwa kafin daga bisani a wallafa wani bangare na abin da suka cimma matsaya a kai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.