Amurka-Afghanistan

Taliban za ta mayar da Afghanistan saniyar ware - Amurka

 Sakataren harkokin wajen Amurka, Anthony Blinken.
Sakataren harkokin wajen Amurka, Anthony Blinken. JIM WATSON POOL/AFP/File

Amurka ta yi gargadin cewa  Afghanitsan za ta kasance saniyar ware , idan har kungiyar Taliban ta karbe mulkin kasar da karfin bakin bindiga.

Talla

Sakataren harkokin wajen Amurka, Anthony Blinken ne ya yi wannan furuci a yayin da ya gana da manema labarai a India, inda ya kai ziyarar aiki a karon farko.

Blinken ya ce ba shakka, kasar Afghanistan da ba ta girmama hakkin dan adam ba, tana kuma aikata ta’asa ga al’ummarta, za ta zama saniyar ware.

Wadannan kalaman nasa na zuwa ne a daidai lokacin da wata tawaga mai karfi ta kungiyar Taliban ta ziyarci birnin Beijin na kasar China, inda ta tabbatar wa da Chinan cewa, kungiyar ba za ta bari a yi amfani da Afghanistan a matsayin sansanin kulla munakisa ga wata kasa ba.

Tawagar wadda akwai daya daga cikin wadanda suka assasa kungiyar Taliban, Mulla Abdul Ghani Baradar, ta isa China don tattaunawa, a daidai lokacin da kungiyar ta Taliban ke dirar mikiya a sassan Afghanistan, ciki har da iyakar kasar da China.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.