Jacob Desvarieux na kungiyar Kassav ya mutu bayan kamuwa da covid 19

Mawakan kungiyar Kassav'.
Mawakan kungiyar Kassav'. DR

Fittacen makadin Guita da aka sani da Jacob Desvarieux  na kungiyar Kassav ya rasu jiya juma’a bayan kamuwa da cutar covid 19.

Talla

Marigayi Jacob Desvarieux na daga cikin mutanen da suka kafa kungiyar ta Kassav da ta yi suna a Duniya kama da shekarar  1980.

Jacob Desvarieux, a shekara ta  2007.
Jacob Desvarieux, a shekara ta 2007. © RFI / Edmond Sadaka

Jacob Desvarieux ya rasu ya na mai shekaru  65 ,an kwantar da shi asibiti tun ranar 12 ga watan yuli.

Shugaban Faransa Emmanuel Macron na daga cikin mutanen da suka aika da sakonni nuna alhini yan lokuta da sanar da mutuwar  fittacen makadin guitar na kungiyar ta Kassav  Jacob Desvarieux.

Daya daga cikin wakokin su ta zagaya Duniya itace  Swe Bwa a shekara ta alip 1987.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI