WHO-Coronavirus

Karin sabbin na'ukan annobar Covid-19 na nan tafe - Tedros

Tedros Adhanom Ghebreyesus, shugaban hukumar lafiya ta duniya, WHO.
Tedros Adhanom Ghebreyesus, shugaban hukumar lafiya ta duniya, WHO. AP - Laurent Gillieron

Hukumar lafiya ta duniya ta ce bullar sabon nau’in cutar Covid -19 da ake wa lakabi da Delta, wani jan kunne ne ga duniya da ta gaggauta dakile shi kafin ya sauya fasali zuwa wani abu mai hatsarin gaske

Talla

Nau’in cutar na Delta mai saurin yaduwa da aka fara ganowa a Indiya ya yadu zuwa kasashe 132 na duniya a cewar hukumar lafiyar ta duniya.

Shugaban hukumar  Tedros Adhanom Ghebreyesus ya kara da cewa ya zuwa yanzu, na’ukan cutar har 4 sun bayyana, kuma wasu ma na nan tafe muddin cutar za ta ci gaba da yaduwa.

Annobar Korona, wadda ta samo asali daga kasar China, ta kashe mutane sama da miliyan 4 a fadin duniya ya zuwa yanzu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.