Bakin-haure

An ceto sama da 'yan cirani 400 daga tekun Mediterranean

Jirgin ruwan agaji na  Ocean Viking, mai ceto 'yan cirani a teku.
Jirgin ruwan agaji na Ocean Viking, mai ceto 'yan cirani a teku. AP - Fabio Peonia

Wasu kungiyoyi masu zaman kansu na kasa da kasa sun ce sun yi nasarar ceto wasu ‘yan cirani 400 a gabar tekun Mediterranean bayan da jirgin da suke ciki ya nutse da su.

Talla

Kungiyoyin da suka yi wannan aikin hadin gwiwar sun hadar da SOS Mediterranee da Sea Watch da kuma ResQship, inda suka ce jirgin su da ke aikin ceto a gabar ruwan ne ya yi nasarar ceto mutanen, bayan da suka hangi jirgin ‘yan ciranin da ke yunkurin tsallakawa turai ya fara tangal tangal a ruwa.

Ta cikin sakon hadin gwiwar da suka wallafa a shafin su na Twitter kungiyoyin sun ce sun ceto ‘yan ci ranin su 400, yayin da tuni aka mika su asibiti don fara karbar agajin gaggawa.

A cewar kungiyoyin wannan shine karo na uku cikin kwanaki uku da suka yi aikin ceto mutanen da ke yunkurin tsallakawa turai ta barauniyar hanya, wadanda kuma jirgin su ya kife a kan tekun.

Kungiyoyin suka ce cikin watanni shidan farko na wannan shekara mutane dubu 1 da 146 ne suka hallaka a tekun, a yunkurin su na tsallkakwa turai, yayin da kuma suka ceto mutanen dubu 30 da ran su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.