Duniya-Coronavirus

Halin da kasashen duniya ke ciki game da Korona

Wasu jami'an yaki da cutar Korona
Wasu jami'an yaki da cutar Korona REUTERS - STRINGER

A yayin da kasashen duniya ke daukar sabbin matakan yaki da cutar Covid-19, China ta killace miliyoyin mutane a gidajensu da zummar dakile sake barkewar cutar mafi muni cikin watanni.

Talla

Yanzu haka China ta sake kaddamar da wani shirin yi wa miliyoyin mutane gwajin annobar Korona tare da daukar matakin takaita tafiye-tafiye.

Nan gaba kadan Jamus za ta yi wa mutanenta rigakafin cutar a zango na uku musamman dattijai masu yawan shekaru.

A can birnin Sydney kuwa, sojojin kasar ne suka mamaye tituna domin tilasta wa jama’a zaman gida na dole, yayin da a Hong Kong aka wajabta wa ma’aikatan gwamnati da malaman makarantu da ma’aikan jinya yin rigakafin annobar.

A wani labarin kuma, a karon farko Iran ta samu adadin mutane dubu 37 da suka harbu da Korona a cikin kwana guda, yayin da shugaban Faransa Emmanuel  Macron ya hau kan shafukan sada zumunta, yana watsi da labaran karyar da aka yi ta yadawa game da rigakafin cutar.

Ita kuwa Libya, kira ta yi ga jama’arta da su fito domin karbar allurar rigakafin da ta karba daga China.

Hukumar Yaki da Yaduwar Cutuka a Afirka ta ce, halin da ake ciki a nahiyar, ya yi kama da wanda kasar India ta fuskanta, sakamakon yawan mutanen da ke kamuwa da cutar Covid-19, yayin da a hannun daya asibitoci ke fama da karancin kayan aiki.

Kawo yanzu jumullar mutane miliyan 4 da dubu 22 da 765 aka tabbatar da mutuwarsu a sassan duniya a dalilin wannan shu’umar cuta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.