Afghanistan-Taliban

Sama da mutane 40 aka kashe a rikicin Afghanistan

Sojojin sa kai dake yakar taliban a yankin ’Hérat, rana10 yuli 2021.
Sojojin sa kai dake yakar taliban a yankin ’Hérat, rana10 yuli 2021. REUTERS - JALIL AHMAD

Majalisar Dinkin Duniya ta ce akalla mutne 40 ne suka mutu, sama da 100 suka ji rauni a cikin sa’o’i 24, sakamakon fada da ake gwabzawa tsakanin dakarun Afghanistan da na Taliban a yankin kudancin kasar, a yayin da hukumomin suka bukaci farar hula su fice daga yankunan da ake rikici. 

Talla

A wani sako da ta wallafa a shafinta na Twitter, Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana  damuwa game da halin da farar hular birnin Lashkar Gah, babban birnin  Lardin Helmand ke ciki, ta na mai bukatar kawo karshen rikici a biranen kasar.

Wata tashar radio a birnin ta ce, an zafafa bai wa hammata iska ne tun wayewar  safiyar Talatar nan, 3 ga watan ogustan 2021  inda jiragen saman yakin Afghanistan suka yi luguden wuta a yankunan da mayakan Taliban suka mamaye, haka kuma rikici na ci gaba da kazancewa a kusa da gidan yarin birnin, da kuma wani gini  da ke dauke da shelkwatar ‘yan sanda da hukumar leken asiri.

 A cikin ‘yan kwanakin nan, dakarun Amurka sun zafafa ruwan wuta ta sama a fadin kasar, a kokarin da suke na dakile hare-haren da ‘yan Taliban ke ci gaba da kai wa.

Kwace birnin Lashkar Gah zai zame wa gwamnatin Afghanistan wani mummunan asara da tashin hankali, duba da alwashin da ta sha na kare dukkan biranen kasar ta kowane hali, bayan da akasarin kauyuka da alkaryun kasar suka shiga hannun ‘yan Taliban.

Tun da farko hukumomi sun ce, kungiyar Taliban ta karbe gwamman tashoshin radio da talabijin na birnin, inda ta bar guda daya tilo mai goyon bayan muradanta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI