Iran-Ra'isi

Sabon shugaban Iran, M. Raissi zai fuskani takunkuman Amurka

sabon shugaban Iran  Ebrahim Raisi a bagaren dama, na karbar takardar amincewa da zabensa daga jagoran juyin juya halin musuncin kasar ayatollah Ali Khamenei  daga Dama. 03-08-2021
sabon shugaban Iran Ebrahim Raisi a bagaren dama, na karbar takardar amincewa da zabensa daga jagoran juyin juya halin musuncin kasar ayatollah Ali Khamenei daga Dama. 03-08-2021 VIA REUTERS - OFFICIAL KHAMENEI WEBSITE

A yau talata ne aka rantsar da mai tsatsauran ra’ayin kare juyin juya halin musuluncin kasar Iran, Ibrahim Raïssi, kan karagar shugabancin kasar Iran.Raïssi ya bayyana cewa, gwamnatinsa za ta yi iya yinta, wajen ganin ata kawo karshen  takunkuman kariyar tattalin arizikin da kasar Amruka ta kakaba mata, ba tare da ta nemi  taimakon kasashen ketare, wajen sake farfado da tattalin arizikin kasar  da suka fuskanci koma baya ba. 

Talla

Tsohon shugaban hukumar  shara’ar kasar, Ibrahim Raïssi, mai shekaru 60 a duniya,  yau ne a hukumance ya karbi rantsuwar  fara  aikin wa’adin mulkin shekaru 4, bayan tabbatar da zabensa, da babban jagoran kare juyin juya halin mulkin musuluncin kasar Ayatollah Ali Khamenei ya yi.

A lokacin da yake jawabi bayan rantsar da shi, M Raissi ya ce zai yi iya kokarin ganin an  cire wa kasar  miyagun takunkuman kariyar tattalin arizikin rashin adalci  da Amurka ta dora wa kasar, sai dai ya kara da cewa, ba za su taba mika wuya ba su watsar da muradun kasar a gaban  kasashen ketare .

Mutumen da ya lashe zaben shugabancin kasar ta Iran, M Raïssi, ya gaji shugaban kasar da ya bar gado mai  ra’ayi tsak-tsaki Hassan Rohani ne, wanda a shekara ta 2015 ya cimma yarjejeniyar nukliyar  da manyan kasshen duniya, bayan share tsawon shekaru ana kai ruwa rana a kai.

Sai dai a 2018 kasar Amruka ta yi watsi da yarjejeniyar, inda ta sake mayar da jerin takunkuman da yarjejeniyar ta  daukewa  kasar  ta Iran, bisa zummar sake jefa kasar ta Iran cikin mawuyacin halin kariyar tattlin ariziki.

M. Raïssi ya ce, muna tsammanin harakokin tattalin arizikin al’umma ya ja baya, wannan kuma na faruwa ne sakamakon matsin lambar makiya, da kuma kasawa da matsalolin da ake fuskanta na cikin gida  

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.