Majalisar Dinkin Duniya-Yanayi

Matsalar gurbatar muhalli na barazana ga hakkin dan adam-MDD

Tekuna da koguna na bushewa sanadiyyar sauyin yanayi.
Tekuna da koguna na bushewa sanadiyyar sauyin yanayi. AMOS GUMULIRA AFP/File

Hukumar kare hakkin dan adam ta majalisar dinkin duniya, ta yi gargadin cewa gurbacewar muhalli da canjin yanayi, na tasiri wajen kara rura wutar tashe-tashen hankula a fadin duniya, matsalar da ta ce nan kusa za ta zama kalubale mafi girma ga kare hakkin dan adam.

Talla

Shugabar hukumar ta UNHCR Mitchel Bachlete ta yi wannan gargadi ne a yayin da take jawabi wurin bude taron kasa da kasa kan kare hakkin dan adam kashi na 48 a birnin Geneva, inda ta ce yanzu haka gurbatar yanayi da muhalli, sare dazuka, da kuma bacewar halittu daga doron kasa sun dade da zama matsalolin da ke kazanta tashe-tashen hankula, zaman tankiya, da kuma rashin daidaito tsakanin mutane a sassan duniya, lamarin da ya tagayyara miliyoyin jama’a.

A cewar Bachelete halin da ake ciki ya zama abin tsoro ne, ganin yadda akasarin kasashe ba sa daukar matakan da suka dace wajen kawo karshen matsalar.

Bachelete ta kara da cewar tuni matsalolin na gurbatar muhalli da canjin yanayi suka fara dakile  jerin hakkokin dan adam da suka hada da samun isasshen abinci, ruwa, ilimi, gidaje, lafiya, ci gaba, har ma da rayuwar kanta.

Zalika gurbacewar muhallin galibi yafi cutar da al’umomin kasashe matalauta sakamakon rashin karfinsu na daukar matakan ware-ware matsalolin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.