Kafafen sada zumunta

Kafofin sada zumunta na duniya sun daina aiki

Miliyoyin mutane ke amfani da shafukan sada zumunta a sassan duniya.
Miliyoyin mutane ke amfani da shafukan sada zumunta a sassan duniya. OLIVIER DOULIERY AFP/File

Kafafen sada zumunta na Facebook da Instagram da WhatsApp sun tsaya cik a wannan Litinin, lamarin da ya shafi miliyoyin masu amfani da su, a dai dai lokacin da manyan kafafen ke fuskantar matsin lamba a game da tasirinsu kan matasa da kuma yadda ake yada labaran karya.

Talla

Na’urar bibiya ta tsaro ta nuna yadda matsalar ta shafi mutane da dama da ke amfani da kafofin sada zumuntar, musamman a birnin Washington na Amurka da kuma Paris na kasar Faransa.

Mai Magana da yawun kamfanin Facebook, Andy Stone a shafinsa na Twitter ya wallafa cewa, suna sane da matsalar da ta kunno kai ta gaza shiga manhajojin kan wayar salula, amma suna kokarin shawo kan matsalar nan bada jimawa ba.

Wannan katsewar na zuwa ne kwana guda bayan wata mai tseguntawa ta ziyarci wani gidan talabijin na Amurka don bayyana yadda ta bankado wasu takardu ga hukumomi da ke zargin kamfanin Facebook da rura matsalar nuna tsana da kuma gurbata lafiyar kwakwalwar kanana yara.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI