Amurka-Faransa

Blinken zai gana da Le Drian kan takaddamar Amurka da Faransa

Sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken yayin ganawarsa da ministan wajen Faransa Jean-Yves Le Drian.
Sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken yayin ganawarsa da ministan wajen Faransa Jean-Yves Le Drian. Andrew Harnik POOL/AFP

Sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken na gudanar da ziyara a Faransa don halartar taron kungiyar Habaka tattalin Arziki da Samar da ci gaba wato OECD da ke gudana a birni Paris. Ziyarar dai na zuwa a daidai lokacin da alaka ta yi tsami sosai tsakanin kasashen biyu bayan da Faransa ta yi asarar kwangilar kera wa Australia jiragen ruwan yaki a kan bilyoyin kudade.

Talla

A yau talata aka shirya ganawa tsakanin Antony Blinken da takwaransa na Faransa Jean-Yves Le Drian domin ci gaba da tattaunawa kan yadda kasashen biyu za su dawo da cikakkiyar yarda a tsakaninsu bayan soke wannan kwangila ta kera jiragen ruwan yaki da aka kulla tsawon shekaru tsakanin Faransa da Australia.

Ko a makon da ya gabata Mataimakiyar Sakataren Wajen Amurka mai kula da kasashen Turai Karen Donfried, ta ce tabbas yarjejeniyar da aka kulla tsakanin Amurka, Birtaniya, da kuma Australia, ta haifar babbar sabaninsu tsakaninsu da Faransa.

Bayan barewar wannan kwangila, shugabannin kasashen biyu Emmanuel Macron da kuma Joe Biden sun tattauna ta wayar tarho, yayin da bayan komawarsa, jakadan Faransa a birnin Washington ya gana da Sakataren waje Blinken da kuma mai bai wa shugaba Biden shawara kan sha’anin tsaro Jake Sullivan.

To a jajibirin wannan ziyara ta Blinken, jaridar New York Times ta ce har yanzu Faransa na cikin fushi dangane da faruwar wannan lamari, to sai dai  Washington Post ta ce Amurka na iya kokarinta don dawo da yarda a tsakanin kasashen biyu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI