Rasha-Turai

Duniya na ganin tashin farashin iskar gas mafi kololuwa cikin shekaru 30

Tukwanen bututun Iskar gas da ke rarrabawa nahiyar Turai.
Tukwanen bututun Iskar gas da ke rarrabawa nahiyar Turai. PACO SERINELLI AFP/Archivos

Farashin iskar gas na ci gaba da tashin gwauron zabi a sassan duniya, musamman a Kasashen Tarayyar Turai da kuma Birtaniya, bayan da tuni kasashen Africa suka yi nisa a fuskantar makamanciyar matsalar da ta kai karuwar farashin da kashi 100 bisa 100.

Talla

Duk da cewa kasashen Turai na cikin jerin wadanda ke fama da matsi bayan tashin farashin iskar ta gas da kashi 25 cikin dari, shugaba Vladmir Puttin na Rasha ya dora alhakin tashin farashin akan Tarayyar Turai.

Rahotanni sun ce ana sayar da iskar gas a kusan dukannin kasashen turai kan yuro 145 da centi 19 yayinda ake sayar da shi a Amurka kan dala 347 da centi 27 farashin da ba a taba gani ba sama da shekaru 30 da suka gabata.

Ko da ya ke Turai ta yi watsi da zargin na Putin, amma wasu bayanai na cewa da gan gan wasu kasashe ke boye iskar ta gas da biyan bukatunsu na radin kai.

Yayin zantawarsa ta kai tsaye a gidan talabijin, Shugaba Putin ya yi watsi da zarge-zargen da ke cewa da hannun Rasha a haddasa tsadar isakar ta gas a Turai.

Rashan da Tarayyar Turai dai na zargin juna da datse bututun gas din da ya sada kasar da Jamus, wanda kusan ta shi ne dukannin kasashen turai ke samun gas din.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI