Amurka -Rashawa

An samu wasu iyaye da laifi a badakalar samun gurbi a jami'o'in Amurka

Daya daga cikin iyayen dalibai da kotun Amurka ta samu da laifin bada cin hanci don samarwa 'ya'yansu gurbi a jami'o'in Amurka, Tsaohon mai gidan Chacha Gamal Abdelaziz da mai da 14 ga watan Satumba 2021.
Daya daga cikin iyayen dalibai da kotun Amurka ta samu da laifin bada cin hanci don samarwa 'ya'yansu gurbi a jami'o'in Amurka, Tsaohon mai gidan Chacha Gamal Abdelaziz da mai da 14 ga watan Satumba 2021. REUTERS - BRIAN SNYDER

Kotun Amurka ta samu wasu iyayen dilabai da suka fara gurfana kan badakalar neman gurbin shiga kwalejin Amurka da laifin bada cin hanci don shigar da 'ya'yansu manyan jami'o'i.

Talla

Alƙalai a Boston, Massachusetts sun sami attajiri John Wilson, mai shekaru 62, da tsohon shugaban gidan caca Gamal Abdelaziz mai shekaru 64, da laifin bada cin hanci da zamba bayan shari'ar makwanni huɗu.

Akwai tsakanin wasu mutane 50 da ake tuhuma kan wannan lamari kan yadda attajiran Amurka ke amfani da kudinsu wajen samawa ‘ya’yansu manyan kwalejoji.

Wasu fitattun shirya fina-finai irinsu Lori Loughlin da Felicity Huffman sun kasance manyan fitattun mutane da suka fuskanci hukunci a gagarumin shari'ar badakalar da akayiwa lakabi da "Operation Varsity Blues."

'Yar wasan "Full House" Loughlin ta yi zaman gidan yari na watanni biyu a bara bayan da ita da mijinta suka yarda sun biya $ 500,000 don samun gurbin shigar' daya'yansu mata biyu a Jami'ar Kudancin California.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI