Masanin kimiyar nukiliyar Pakistan ya rasu bayan kamuwa da Covid 19

Masanin kimiyar Pakistan  Abdul Qadeer Khan.
Masanin kimiyar Pakistan Abdul Qadeer Khan. Reuters

Daya daga cikin masanan Pakistan da ya samar da makamin Nukiliya Abdul Qadeer Khan dake a matsayin gwarzo a kasar ya rasu ya na mai shekaru 85. Sanarwar da hukumomin kasar suka fitar a yau lahadi,masanin ya share lokaci ya na jiya bayan kamuwa da cutar covid 19.

Talla

Abdul Qadeer Khan na daga jarumai na kasar ,duk da zargin da aka yi  da fallasa bayanan siri  dangane da hanyoyin hada makami nukiliya  zuwa kasashen Iran,Koriya ta arewa da Libya.

Masanin kimiyar nukiliyar Pakistan Khan
Masanin kimiyar nukiliyar Pakistan Khan Aamir QURESHI AFP/File

Shugaban kasar ta Pakistan  Arif Alvi a wani sako ta kaffar twitter ya bayyana alhinin sa tareda isar da sakon ta’azziya zuwa iyalan mammacin da yan  kasar ga baki daya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI