Macron-Taliban

Macron ya gana da shugaban Tajikistan a kokarin kalubalantar Taliban

Ganawar shugaban Tajikistan Emamali Rakhmon da takwaransa na Faransa Emmanuel Macron.
Ganawar shugaban Tajikistan Emamali Rakhmon da takwaransa na Faransa Emmanuel Macron. REUTERS - GONZALO FUENTES

Shugaba Emmanuel Macron na Faransa ya karbi bakoncin takwaransa na Tajikistan Emamali Rakhmon don tattaunawa kan yadda za su yi aiki tare don tunkarar kalubalen da ke tunkaro nahiyar Asiya bayan kwace mulkin da Taliban ta yi a Afghanistan kusan watanni 3 da suka gabata.

Talla

Fadar Elysee ta aikewa da shugaban na Tajikistan goron gayyata don tattaunawar da ke da nufin lalubo hanyoyin magance rikicin yankin bayan kwace ikon Taliban da Afghanistan wadda ke matsayin makwabciyar Tajikistan.

Shugaba Emmanuel Macron na da yakinin cewa, kasashen makwabta za su taka muhimmiyar rawa wajen magance rikicin Afghanistan musamman shi shugaba Emomali Rakhmon da ke kan madafun iko tun shekarar 1992.

Tajikistan dai ita ke iyaka mafi girma tsakaninta da Afghanistan fiye da kasashen Iran da Pakistan, ka zalika it ace kasa mafi musanci da Kabul wadda kuma ke kalubalantar salon kamun ludayin Taliban, wanda ke ci gaba da fuskantar kakkausar suka daga manyan kasashen Duniya musamman kan hana mata ‘yancin walwala.

Yayin ganawar shugaba Emmanuel Macron ya bukaci Tajikistan ta taimakawa tsaron duniya wajen tabbatar da zaman lafiya tare da ‘yancin al’ummar Afghanistan.

Shugaba Rakhmon wanda tsawon shekaru ya ke yaki da matsalar tsaurin akidar islama tare da yakar masu fafutukar tabbatar da bin tsarin musulunci ya ce kasarsa a shirye ta ke ta taiumakwa Faransar wadda ya kira a matsayin kawa garesu.

Duk da yadda makwabtan Afghanistan ciki har da Uzbekistan suka mara baya ga Taliban Tajikistan na matsayin babban abokiyar gaba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI