Muhalli

Duniya na dakon ganin ko kasashen G20 za su cika alkawarin dakile sauyin yanayi

Ministan kula da albarkatun noma, da ruwa da kuma muhalli na kasar Saudiya AbdulRahman Al-Fadhli da kuma Roberto Cingolani ministan muhalli na kasar Italiya a birnin Rome.
Ministan kula da albarkatun noma, da ruwa da kuma muhalli na kasar Saudiya AbdulRahman Al-Fadhli da kuma Roberto Cingolani ministan muhalli na kasar Italiya a birnin Rome. © G20Italy/Handout via REUTERS

Yayin da kasashe kusan 200 ke hallara a birnin Glasgow na Scotland domin ganawa a babban taron da Majalisar Dinkin Duniya za ta jagoranta kan matsalar Sauyin Yanayi da za a fara ranar Lahadi, hankula sun karkata kan birnin Rome, inda taron G20 da za a kammala a wannan ranar zai fayyace aniyar kasashen duniya masu karfin tattalin arziki wajen cika alkawarin dakile matsalar ta dumamar yanayi.

Talla

Za a iya cewa karo na farko kenan da batun dumama ko sauyin yanayi ke mamaye taron kasashen na G20, zalika karon farko kenan da shugabannin kasashen mafiya karfin tattalin arziki za su wuce kai tsaye zuwa babban taron Majalisar Dinkin Duniya kan sauyin yanayin bayan kammala nasu taron na masu kumbar susa.

Ana dai sa ran shugabannin kasashen fiye da 120 ne za su halarci taron na kasa da kasa kan dumamar yanayi a bana, cikinsu har da na China, Amurka, Indiya, Rasha da kuma kasashen EU, wadanda ke da kashi 80 cikin 100 na karfin tattalin arzikin duniya, yayin da kuma suke fitar da kashi 80 cikin 100 na hayakin dake gurbata muhalli.

Manyan batutuwan da za su mamaye taro kan suyin yanayin na bana dai za su hada da cika alkawuran daukar matakan rage matsalar, da kuma kara yawan kudaden tallafawa kasashe matalauta, daga dala biliyan 100 a duk shekara zuwa dala biliyan 125, domin takaita musu tasirin matsalar gurbacewar Yanayin da muhalli.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI