Turkiya-Amurka

Erdogan ya gargadi Amurka kan yiwa Turkiya katsalandan a harkokinta

Shugaba Recep Tayyip Erdogan na Turkiya.
Shugaba Recep Tayyip Erdogan na Turkiya. Adem Altan AFP/Archivos

Shugaban Turkiya Recep Tayyip Erdogan ya gargadi Amurka cewar tana gaf da rasa daya daga cikin manyan kawayen ta muddin ta ci gaba da yiwa kasar sa katsalandan.

Talla

Erdogan wanda ake saran ya gana da shugaba Joe Biden nan da makwanni biyu masu zuwa ya ce ba za su bari Amurka ta ci gaba da nuna musu kiyayya ba, bayan shugaba Biden ya bayyana cewar Turkiya da aikata kisan kiyashi a Armenia.

Dangantaka tsakanin Amurka da Turkiya ta yi tsami tun bayan da shugaba Biden ya maye gurbin Donald Trump bayan zaben 2020.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.