Mu Zagaya Duniya

Halasta kudaden haram a turai daga yan Afrika

Sauti 20:50
halasta kudaden  haram
halasta kudaden haram © iStock

Kotu a Faransa na tuhumar ‘ya da kuma surukin shugaban kasar Congo-Brazzaville Denis Sassou-Nguesso da mallakar kadarori ciki har da gidaje wanda ake iya fassarawa a matsayin laifin halasta kudaden haram.Shekaru 7 bangaren shari’a ya share yana gudanar da bincike dangane da wannan batu, inda a cikin watan maris da ya gabata suka ambaci sunan Wilfrid Nguesso, yayin da a wannan karo aka bayyana Julienne Sassou-Nguesso da mijinta Guy Johson da hannu wajen halasta kudaden na haram.