Ali Nuhu ya shigar da karar Adam Zango a kotu
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Fitaccen jarumin fina-finan Kannywood na Hausa, Ali Nuhu ya shigar da karar takwaransa a harkar fina-finan, Adam Zango bisa zargin sa da bata masa suna.
Jaridar Daily Trust ta ce, Ali Nuhu ya maka Zango a gaban kotun USC da ke unguwar Fagge ta jihar Kanon Najeriya a ranar Alhamis.
A cikin sammacin da ta fitar, kotun ta bukaci Zango da ya bayyana a gabanta a ranar Litinin mai zuwa, wato 15 ga watan nan na Afrilu da misalin karfe 8:30 na safe agogon kasar.
Jaridar Daily Trust ba ta yi bayani ba kan irin bata sunan da Ali Nuhu ke zargin Zango da yi masa.
Fitattun jaruman biyu sun shafe tsawon watanni suna takun-saka da juna, yayinda yunkurin sasanta su ya ci tura.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu