Iran-Ra'isi

Sabon shugaban Iran na da ra'ayin rikau kan nukiliyar kasar

Zababben shugaban Iran, Ebrahim Raisi
Zababben shugaban Iran, Ebrahim Raisi AP - Vahid Salemi

Kwanaki uku bayan lashe zaben shugabancin Iran, Ebrahim Ra'isi mai ra’ayin kare juyin juya halin musuluncin kasar, ya ce ba zai ci gaba da tattauna batun samar da nukliyar kasar a cikin son-rai, haka kuma  ba zai gana da shugaban Amruka Joe Biden ba.

Talla

Ra'isi ya kasance makusanci ga jagoran juyin juya halin musuluncin kasar, Ayatullahi Ali Khamenei, bayan haka kuma a lokacin wani taron manema labarai na farko tun bayan zaben sa kan shugabancin Iran,  ya ce babu wani tarnaki da zai hana shi sake maida huldar diflomasiya da aka dakatar tun cikin 2016 tsakanin masarautar 'yan sunni ta kasar Saudi Arabiya, babbar abokiyar gabar kasar ta Jamhuriyar Musulunci ta Iran 'yar Shi’a.

Haka kuma a jawabin ya jadda cewa, a kullum aikinsa shi ne kare hakkin dan adam a yayin da kasar Amurka da kungiyoyi masu zaman kansu na  kasashen yammaci da dama ke zargin sa da zama wanda ke da alhakin azabtarwa tare da kisan mummuke, da kuma tashe-tshen hankulla da aka aikata a tsawon lokacin da ya dauka yana  rike da akalar tafiyar da fannin shara’ar kasar.

Shugaba ne a fannin hukumomin shara’ar kasar Iran, a baya Raïssi, da ya kamata ya fara aikin shugabancin kasar Iran a cikin watan Agustan mai zuwa,  ya yi nasarar lashe zabensa ne da kimanin kashi 62% na yawan kuri’un da aka kada,  a zaben da ya ciri tuta daga cikin zabukan da ba su samu halartar masu zabe da yawa ba.

Duk da cewa an san shi mutun ne mai ra’ayin rikau, kamar sauran takwarorinsa masu ra’ayin kare jamhuriyar Musulunci, furucinsa a taron manema labaran na farko ya nuna cewa, akwai jan-aiki ga masu son ganin Iran ta mika wuya ga muradun kasashen yammaci da Amruka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.