Yemen - Houthi

Dakarun Yemen da 'yan tawaye sama da 100 suka mutu a wani sabon rikici

Sabon fada tsakanin mayakan 'yan tawayen Houthi da dakarun Yemen yayin sanadin mutuwar mayaka fiye da 40.
Sabon fada tsakanin mayakan 'yan tawayen Houthi da dakarun Yemen yayin sanadin mutuwar mayaka fiye da 40. © Getty Images

Rikici tsakanin ‘yan tawaye da dakarun gwamnati Yemen ya yi sanadin mutuwar mutane 111 a yankin Magrib a cikin kwanaki 3, kamar yada majiyoyi na kusa da gwamnatin suka bayyana, biyo bayan wani sabon ba-ta – kashi da ya barke a tsakaninsu.

Talla

Majiyoyin sun shaida wa kamfanin dillancin labaran Faransa cewa yakin da ya sake barkewa a tsakanin ranar Alhamis zuwa Lahadi ya janyo mutuwar dakarun gwamnati 29 da nan ‘yan tawaye 82.

Tun a watan Fabrairu ‘yan tawayen Huthi, masu samun goyon bayan Iran suka kara azama a kokarinsu na kwato yankin Magrib, wuri na karshe mai mahimmanci da ke hannun gwamnati, lamarin da ya yi sanadin mutuwar daruruwan dakaru daga dukkan bangarori.

Yakin nan Yemen ya  kazance ne  a shekarar 2014, lokacin da ‘yan tawayen Huthi suka karbe babban birnin kasar Sana’a, abin da ya sa Saudiyya ta kai gwamnatin dauki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.