Isra'ila-Palestine

Firaministan Isra'ila ya sha kashi a majalisar dokoki

Firaministan Isra'ila Naftali Bennett
Firaministan Isra'ila Naftali Bennett Menahem KAHANA AFP

Firaministan Isra’ila Naftali Bennett ya gamu da gagarumin koma-baya a wannan Talatar saboda yadda ‘yan Majalisar kasar suka ki amincewa da matakin tsawaita dokar da ta haramta bayar da takardun shaidar zama dan-kasa ga Falasdinawan da ke rayuwa a yankin Yamma ga Kogin Jordan da kuma Zirin Gaza.

Talla

Tun a shekarar 2003 aka kirkiri wannan doka a lokacin da Falasdinawa suka gudanar da zanga-zangar adawa da mamayar Yahudawa, yayin da dokar ta samu goyon baya daga wani bangare duk da cewa, masharhanta sun caccake ta, suna masu alakanta ta da nuna wariya ga tsirarun Larabawan Isra’ila.

Firaminista Bennett mai ra’ayin rikau, na goyon bayan sabunta wannan doka wadda ta haddasa rarrabuwar kawuna tsakanin mambobin jam’iyyarsa ta hadaka mai karamin rinjaye a Majalisar Dokokin Isra’ila mai kujeru 120.

A wata doguwar tattaunawar da suka shafe dare suna yin ta, mambobin jam’iyyar hadakar  ta Benneth sun yi nufin cimma matsaya guda domin goyon bayan tsawaita dokar haramcin bai wa Falasdinawan takardun shaidar zama ‘yan kasa domin sake yin tozali da iyalensu a Isra’ila.

Sai dai wannan matsayar tasu ta wargaje ganin yadda daya daga cikin mambobin jam’iyyar hadakar, Amichai Chikli, ya mara wa ‘yan adawa wajen kada kuri’arsa ta kin amincewa da tsawaita dokar.

Kuri’ar Chikli ce ta sa jam’iyyar hadakar mai mulki da kuma bangaren ‘yan adawa suka yi kan-kan-kan da kuri’u 59 ga kowannensu, abin da ke nufin cewa, wannan doka ta kawo karshe daga yau Talata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.