Afghanistan

IS ta dauki alhakin hari kan fadar shugaban Afghanistan

Wata mota da ta kone a sandiyar harin rokokin da aka kai wa fadar shugaban kasar Afghanistan
Wata mota da ta kone a sandiyar harin rokokin da aka kai wa fadar shugaban kasar Afghanistan AP - Rahmat Gul

Kungiyar mayakan IS ta dauki alhakin harin ta’addanci a lokacin da ake gudanar da sallar Idi a masallacin gab da fadar shugaban kasar Afghanistan.

Talla

An dai fara jin kararrakin rokoki a dai-dai lokacin da shugaban kasar ke jagorantar sallar Idin bana, abin da ya haifar da fargaba a zukatan al’ummar kasar.

Ya zuwa yanzu dai jami’an tsaro sun tabbatar da cewa an harba makaman rokoki 7  kan fadar shugaban kasar, baya ga harba su a sauran sassan kasar.

Ana zargin mayakan na IS da taimaka wa mayakan Taliban wajen kaddamar da mabanbantan hare-haren ta'addanci a Afghanistan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.