Yemen

Wani gwamna a Yemen ya tsallake rijiya da baya bayan harin da ya kashe mutane 5

Jami'an tsaron Yemen lokacion da suka isa inda aka akai harin bam da mota Aden ranar Lahadi 10/10/21.
Jami'an tsaron Yemen lokacion da suka isa inda aka akai harin bam da mota Aden ranar Lahadi 10/10/21. Saleh Al-OBEIDI AFP

Akalla mutane biyar suka mutu a kasar Yemen, sakamakon wani harin bam da aka kai da mota da nufin hallaka gwamnan lardin Aden, na  gwamnatin da kasashen duniya suka amince da shi, kamar yadda majiyoyin tsaro a suka tabbatar a wannan Lahadi.

Talla

Aden, dake kudancin Yaman, tinga ce ga masu fafutukar neman ballewa, wanda a bara ta shiga hannun gwamnatin, kuma yanki ne da ya dade ana goyawa 'yan tawayen Huthi baya a yakin da aka dade ana fafatawa.

A yayin wannan hari dai, Gwamnan Aden Ahmed Lamlas da Salem al-Socotri, wani minista na gwamnati, duk sun tsallake rijiya da baya a cewar majaiyoyin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI