Media

Ranar Aikin Yan Jaridu ta Duniya

Yayin da yau ake bikin ranar Yan Jaridu ta duniya, Kungiyar da ke kare aikin Jarida, wato Reporters Without Borders, ta baiyana sunayen kungiyoyi da kasashe 40 da ke karan tsaye wa aikin Jarida a duniya.Sanarwar da kungiyar ta bayar, ta baiyana Yan siyasa, shugabanin addini da Yan ta’adda, a matsayin masu musgunawa Yan Jaridu, inda ta ke cewa, wadannan kungiyoyi suna da karfi, kuma suna da hadari, kana kuma sun fi karfin doka a kasashen su.Kungiyar dake da cibiya a birnin Paris na kasar Faransa, ta baiyana shugabanin kasashe 17, a matsayin wadanda ba sa ragawa Yan Jarida, cikinsu harda shugaban kasar China, Hu Jintao, shugaban Iran, Mahmoud Ahmadenajad, shugaba Paul Kagame na Rwanda, da Prime Minista Vladimir Putin na Rasha, da kuma Raul Castro na Cuba.Har ila yau, kungiyar ta zargi shugaban kasar Yemen, da kungiyar Yan Awaren ETA ta kasar Spain, da FARC ta kasar Colombiya, kana kuma da kungiyar Yan ta’adan Philippines, a matsayin masu musgunawa Yan Jaridu.Kungiyar ta ce, yanzu haka an kashe Yan Jaridu tara a cikin wannan shekara ta 2010, yayin da 300 ke garkame a gidan yari.Kungiyar ta fitar da sunayen akasarin kungiyoyin Islaman kasar Iraki daga cikin lissafin, saboda duk da tashin hankalin da ake ci gaba da samu, Yan jaridu ba su zama mutanen da ake hako ba.Daidai lokacin da ake fuskantan zaben shugaban kasar Rwanda na watan Agusta mai zuwa, hukumomin kasar tun bada umurnin tisa keyar dan jarida Robert Mukomboz daga cikin kasar, saboda ya soki shugaba Paul Kagame.Albarkacin wannan rana shugaban kasar Sri Lanka Mahinda Rajapaksa ya bada umurnin sakin dan jaridar kasar da a ka daure na tsawon shekaru 20 a gidan kurkuku, saboda tuhumar aiyukan ta'addanci.