Latin-Amurka

Guguwa dake dauke da ruwan sama ta hallaka mutane 100

Guguwa mai dauke da ruwan sama data ratsa kasashen Lamtin Amurka mai suna Agatha ta hallaka mutane kusan 100
Guguwa mai dauke da ruwan sama data ratsa kasashen Lamtin Amurka mai suna Agatha ta hallaka mutane kusan 100 Reuters

Kusan mutane 100 suka hallaka sanadiyar mahaukaciyar gguguwa mai dauke da ruwan sama data ratsa wasu kasashen Latin Amurka.Lamarin ya fi muni a kasar Guatemala inda akalla mutane 82 suka hallaka, yayin da ta hallaka tara a kasar El Salvador, sannan wasu mutanen takwas suka hallaka a kasar Honduras.Iskar dake dauke da ruwan sama ta karshen mako ta ratsa kasar Guatemala jim kadan bayan da kasar ta fuskanci bala’in dutsen da ya yi aman wuta.Ana saran adadin mutanen da suka hallaka zai karu yayin da aka samu kutsawa yankunan da ruwan ya mamaye, musamman a kasar ta Guatemala. An rada wa wannan mahaukaciyar guguwa dake dauke da ruwan saman suna Agatha, kuma ta dangana da kudancin kasar Mexico.Shugaban kasar ta Guatemala Alvaro Colom ya shaida wa manema labarai cewa kimanin mutane dubu dari da goma sha-biyu (112,000) suke tsere daga gidajensu, sanadiyar aman wuta da dutsen ya yi, da kuma iskar mai dauke da ruwan masa.