GABON
Ana Tsare Da Mutane 13 Saboda Safarar Hauren Giwa A Gabon
Wallafawa ranar:
Mutane 13 na tsare a kasar Gabon saboda samunsu da hannu wajen safarar hauren giwa daga dazukan kasar.Mutanen sun hada da ‘yan kasar Kamaru uku da mutane 10 ‘yan kasar Senegal.A makon jiya ne dai aka kama mutanen da laifin.Wani jamiin Hukumar Gandun Daji na kasar ya fadawa kamfanin Dillancin labaran Faransa cewa akwai yawaitan safarar hauren giwa a kasar.Tun shekara ta 1981 kasar Gabon ta haramta safarar hauren giwa afadin kasar.