Wikileaks
Faransa Zata Toshe Wikileaks a yanar Gizo
Wallafawa ranar:
Ministan Masana’antu na kasar Faransa Eric Besson yau ya bukaci haramta barin bayanai na tonon sililin nan na Wikileaks cikin yanar gizo na faransa.Kasar Amirka tuni ta toshe Wikileaks cikin yanar gizo dake fadin kasar saboda yadda suka warware mata zane a tsakiyar kasuwa.Ministan Masana'antun Faransa Eric Besson cikin wata wasika da ya aikawa Hukumar kula da yanar gizo na Faransa, yace yadda ake tonon sirrin ko kadan bazata sabu ba.Yace Faransa ba zata karbi bakuncin masu tona mata sirri ba, saboda haka akwai bukatar a toshe kafar.