Iraki

Hatsarin Mota Ya Kashe Mutane 17 A Iraki Yau

Taswirar kasar Iraki
Taswirar kasar Iraki rfi

Yau anyi wani mummunar hatsarin mota a kudancin kasar Iraki, inda mutane 17 suka mutu, ciki har da Iraniyawa 14 dake kan hanyar su ta zuwa ziyara Najaf.Wani jamii na Asibitin Hilla yankin Babil dake kudancin Bagadaza Dr. Ali al-Shammari ya fadi cewa mutane 53 sun sami munanan raunuka.Daga cikin masu raunukan 42 masu kai ziyara ne ‘yan shia.