Guinea Conakry

Kotun Koli Ta Amince Da Alpha Conde

Sabon Shugaban Guinea Alpha Condé.
Sabon Shugaban Guinea Alpha Condé. rfi

Kotun Koli dake kasar Guinea yau ta tabbatar da cewa Alpha Conde ne yayi nasaran babban zaben kasar don zama Shugaban kasar bayan gudanar da zabe na farko mai tsabta tun bayan samun ‘yancin kasar.Bayan zaman jira na makonni biyu domin sanin wanda Allah ya baiwa nasara, yanzu haka Kotun Koli dake kasar tace Alpha Conde ne ya dace ya Shugabanci kasar.Alpha Conde mai shekaru 72 dan takaran jamiyyar RPG ya sami kuriu kashi 52% na kuriun da aka jefa a kasar.Alkalin Kotun Mamadou Sylla ne ya fadawa manema labarai sakamakon zaben na karshe.Yace Cellou Dalein Diallo ya sami yawan kuriu kashi 47%.