Cote d’ivoire

Lamurra Na Kara Rinchabewa a Kasar Ivory Coast

Shugaban Ivory Coast Laurent Gbagbo da Alassane Ouattara
Shugaban Ivory Coast Laurent Gbagbo da Alassane Ouattara rfi

Sojan kasar Ivory Coast sun rufe kan iyakokin kasar ta kasa da Sama data ruwa har, babu sauran shige da fice na jama’a da kayayyaki.Yanzu haka kasar na cikin rudani sakamakon ikirarin da Shugaban kasar Laurent Gbagbo yayi na kin sauka daga mulkin ya baiwa wanda ya lashe zaben Shugabancin kasar.Bayanai na cewa Hukumomin kasar zasu yamutsa sautin gidajen Radiyo da Talabijin na kasashen waje dake zantuka gameda kasar.Kazalika bayanan na cewa zasu hana samun dukkan bayanai ta filin jiragen sama na kasar dake Abidjan.Wadannan matakai na zuwa ne bayan da Kotun tsarin mulkin kasar ta ki amincewa da bayanan Hukumar zaben kasar dake nuna cewa Alassane Ouatara na jamiyyar adawa ya lashe zaben Shugabancin kasar.