Israel

Wutan daji ta kashe Mutane 41 a Kasar Israela

Yadda wutar daji ke barna a kasar Israela
Yadda wutar daji ke barna a kasar Israela rfi

Masu ayyukan ceto a kasar Israela na can suna ta kai dauki kan dumbin jamaa da gobara ke yiwa barna yanzu haka bayan ta hallaka mutane akalla 41.Masu aikin kwana-kwana na can suka ta aikin kashe gobaran.Mai magana da yawun ‘yan sandan yankin Micky Rosenfeld ya fadi cewa akwai mutane akalla 16 da suka sami munanan raunuka.Acewar sa an sami kwashe mutane 15,000 daga yankunan garin Haifa, gari na uku mafi girma a Israela, inda gobarar ke ta’adi.Akwai jimillan mutane 250,000a wannan gari.