Kotu Ta Hana Belin Mawallafin Wikileaks
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Bayanai da dimi-dimi na cewa an kama Julian Assange a London, mutumin da ya kirkiro sashen yanar gizo na Wikileaks, saboda zargin da Hukumomin kasar Sweden keyi masa na fyade.‘Yan sandan London suka gayyace shi inda suka kama shi.Bayan ya bayyana gaban Kotun Majistare na City of Westminister yau Kotun taki amincewa daa badashi beli.Assange ya musanta zargin da akeyi masa inda Lauyan sa Mark Stephen ke fadin akwai harkan siyasa wajen tuhumar.A ranar 19 ga watan jiya wata kotun kasar Sweden ta bada sammacin kama Julian Assange saboda zargin sa da yin fyade.Wannan mutun ya dade yana buya saboda kirkiro sashen yanar gizo dake tonon silili yanzu haka da ake kira Wikileaks