France-India
Sarkozy na kammala ziyara Indiya
Wallafawa ranar:
Shugaban kasar Faransa Nicholas Sarkozy ya soki kasar Pakistan saboda barin ‘yan ta'adda suna yadda suke so.Shugaba Sarkozy wanda yake karkare rangadin kwanaki hudu a kasar India, ya yada zango a Mumbai inda ‘yan ta'adda suka kai kazamin hari cikin shekara ta 2008.Yace sam ba abin amincewa bane barin ‘yan ta'adda suna zaune a Pakistan su rika kai hari kasar India ko Afghanistan.Ya bukaci mutan kasar Pakistan da Hukumomin kasar dasu dasu kara kokari wajen yaki da masu aikata laifuka.Shugaba Sarkozy wanda yake tare da matar sa Carla Bruni, da fari sun ajiye furanni a wani wuri inda aka kashe ‘yan sanda 18.