Cancun-Mexico

An Kammala Taro Gameda Dumamar Yanayi Na Duniya

Shugaban kasar Bolivia Evo Morales na wani karamin taro, a Cancun na kasar Mexico
Shugaban kasar Bolivia Evo Morales na wani karamin taro, a Cancun na kasar Mexico rfi

Mahalarta taron duniya gameda batun dumamar yanayi da akayi a Cancun na kasar Mexico sun kusa kaiga nasara a fafutukan da akeyi na tsarkake yanayin sararin duniya daga mummunar gurbacewa.Taron ya kafa komitoci biyu duk da cewa kasar Bolivia ta nuna rashin amincewa da wasu matakai.Yarjejeniyar da aka tsaida sun hada da kafa asusu na kudi Dalan Amirka Biliyan 100 ko kuma Kudin Turai Euro Biliyan 75 domin sauke dukkan alkawurran da aka dauka na taimakawa kasashen da ke cikin wani hali saboda gurbacewar yanayi.