Sweden

Harin Bam A Sweden Ya Kashe Mutun Daya

Lokacin da bam ya tashi a Sweden
Lokacin da bam ya tashi a Sweden rfi

‘Yan Sanda a kasar Sweden na binciken musabbabin wani harin taaddanci inda wani mutun daya ya mutu wasu mutane biyu suka sami raunuka a birnin Stockholm.Bayanai na nuna dan kunar bakin waken ne ya rasa ransa a harin a wannan hari daya tada hankulan jamaa dake hada-hadan sayayyan bukin Kirsimati dake tafe.Ba’a bada bayanin mutumin ba har ya zuwa wannan lokaci.Ganau sunce bam na farko ya tashi ne daga cikin mota, kafin wani bam din ya sake tashi kusa.Wani Jami’in tsaro Anders Thornberg yace idan har ya kasance harin taaddanci ne zai kasance na farko kenan a kasar.