Enahoro

Anthony Enahoro Ya Mutu

Marigayi Anthony Enahoro
Marigayi Anthony Enahoro rfi

Anthony Enahoro mai shekaru 87 ya mutu a Asibitin koyarwa dake Benin.Anthony Enahoro ya kasance a sahun gaba wajen fafutukan neman ‘yancin kan Najeriya cikin shekara ta 1957.Yana cikin kungiyar da sukayi gwagwarmaya na NADECO wadan da suka hurawa Gwamnatin Soja ta Janar Sani Abacha wuta domin ta sauka daga mulki.Tun cikin watan 10 data gabata marigayi Anthony Enahoro ya fadi sumamme aka kwashe shi zuwa asibiti inda yake kwance tun lokacin har yanzu da ya mutu.