Cote d’ivoire

Jean Ping Zai tafi Cote d'Ivoire

Shugaban Hukumar Tarayyar Afrika Jean Ping
Shugaban Hukumar Tarayyar Afrika Jean Ping rfi

Shugaban Hukumar Tarayyar Afrika Jean Ping na kan hanyar sa ta zuwa kasar Cote d’Ivoire  Juma'a domin shiga sasantawa da akeyi gameda rikicin Shugabancin kasar.Mai magana da yawun sa Noureddine Mezni ya fadi cewa Jean Ping zai sadu da bangarorin biyu dake jayayya da juna, wato bangaren Shugaba Laurent Gbagbo da kuma wanda ake cewa shine ya lashe zabe na baya-bayan nan Alassane Outtara.Yace Jean Ping na kasar Algeriya Alhamis, kafin ya tafi Najeriya ya tattauna da Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan wanda shine Shugaban Kungiyar Kasashen Yammacin Afrika mai jimillan kasashe 15.Shi kansa Babban magatakardan Majalisar Dinkin Duniya Ban Kimoon ya nuna fargaban sa cewa fada na iya barkewa a kasar ta Cote d’Ivoire saboda yadda harkoki suka tsaya cik.