Australiya
Jirgin Ruwa Ya Nutse Da Mutane 50 A Australiya
Wallafawa ranar:
AKALLA bakin haure 50 dake neman mafakar siyasa ne ake zaton sun rasa rayukansu, lokacin da kwale kwalen da suke ciki ya kife, sakamakon mummunar yanayi a kasar Australia.Wani likita yace mutane 36 sun samu raunuka, wasu kuma raunin nasu yayi tsanani.Wani shaidar gani da ido a Christmas Island, kusa da inda akayi hadarin, yace cikin wadanda suka rasu harda yara kanana, domin ya ga wani karamin yaro dake sanye da rigar ruwa, amma kuma fuskarsa a kife, a saman ruwa.Mutanen dake tsibirin sun ce, mummunar yanayi da igiyar ruwa, sun hana su kai dauki gab akin.