Kenya

Kotun Kasa Da Kasa Zata Tuhumi Mutane Shida Na Kenya

Uhuru Kenyatta Ministan kudi na kasar Kenya
Uhuru Kenyatta Ministan kudi na kasar Kenya rfi

Uhuru Kenyatta, dan Shugaban kasar Kenya na farko ya nuna bashi da laifin da Kotun kasa da kasa ke zargin sa da aikatawa na kazamin rikicin da yayi sanadiyyar mutuwar mutane da yawa a kasar.Dan shekaru 49 Uhuru Kenyatta wanda yake da mukamin Prime Minista kuma Ministan kudade na kasar, na fuskantar zargi ne na zuga wani gungun ‘yan taadda da ake kira Mungiki domin tada zaune a kasar shekaru uku da suka gabata.Uhuru Kenyatta ya fadawa taron manema labarai a Nairobi cewa akwai shi da kyakyawan suna kuma a duba a gani bai taba aikata wani laifi ba.Yana wadan nan bayanai ne jim kadan bayan Kotun kasa da kasa ta bayyana sunayen mutane shida da zata gabatar dasu gaban kotun domin fuskantar shariar laifukan.Bai ce ga yadda zaiyi bai dan kotun ta gayyace, saidai kawai yace ajira a gani.