Wani Dan Kunar Bakin Wake Ya Kashe Mutane 36 Cikin Masallaci
Wallafawa ranar:
WANI Dan kunar bakin wake, ya tashi Bom a Masallachin birnin Chabahar, dake kasar Iran, abinda ya hallaka mutane 36, ya kuma raunana sama da 50.Bayanan dake zuwa daga kasar, sun nuna cewar wani Dan kunar bakin waken ya tada bom, a Massalachin Imam Hussein, dake kudu maso gabashin birnin.Mataimakin Ministan harkokin cikin gida, Ali Abdullahi, yace bama bamai biyu ne suka tashi a Massalachin, daya bayan daya.Wannan hari na zuwa ne, a Yammacin ranar bikin Ashura, daya daga cikin manyan bukukuwan mabiya Shia, inda dubban mutane kan taru a Masallatan kasar Iran, dan gudanar da ibada.Bayanan da muka samu, lokacin hada wannan rahoto, sun nuna cewar, akalla mutane 36 suka mutu, yayin da sama da 50 suka samu raunuka.Yan Sanda sun sanar da kama wani Dan kunar bakin waken, kafin ya tashi nashi bom din.Babu dai wata kungiya da ta dauki alhakin kai harin.