Niger
Nijar Ta Tura Tandja Gidan Yari
Wallafawa ranar:
Da yammacin jiya ne Hukumomin kasar Nijar suka tura keyar tsohon Shugaban kasar ta Nijar Mamadu Tandja gidan yari daga wani gidan kasaita na Gwamnati da yake tsare.Hukumomin Nijar sun bukaci a cigaba da tsare mata tsohon Shugaban a gidan yari dake garin Kallo mai kimanin nisan kilomita 30 daga Kudancin Yamai.Zargin da akeyiwa tsohon Shugaba sun hada da salwancewar wasu makudan kudade a zamaninsa.