Uganda

Surukin Shugaba Museveni Na Son Bada Hanci

Shugaba Yoweri Museveni na kasar Uganda.
Shugaba Yoweri Museveni na kasar Uganda. rfi

A kasar Uganda, ana zargin wani surukin Shugaban kasar Yoweri Museveni da laifin bada wasu kudade cin hanci ga ‘yan adawa na kudin da suka kai Dolan Amirka 630,000 domin a janye masa daga takaran watan gobe.Francis Atugonza, wanda magajin gari ne kuma mai magana da yawun jamiyyar adawa ta FDC ya fadi cewa surukin Shugaban kasar mai suna Odrek Rwabogo ya yi tallafin kudaden ne a gidan cin abinci ranar biyar ga wannan watan.Mai zargin bashi da wasu karin hujjoji amma kuma ya nunawa manema labarai tattaunawa ta wayan hannu da suka rika yi da surukin Shugaban kasar.Surukin Shugaban kasar ya amsa cewa sun gana da mutumin amma kuma baice ga irin abubuwan da suka tattauna ba.